Janar Oluyede ga sojoji:Ku gama da Bello Turji cikin kwana 30

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Babban Hafsan Sojin ƙasan Nijeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayar da umarni mai ƙarfi ga dakarun haɗin gwiwa na Operations Fansan Yamma da ke yankin Arewa maso Yamma da su ƙara zage damtse da nufin kawo ƙarshen fitaccen jagoran ɗan bindigar nan, Bello Turji, a raye ko a mace nan da kwanaki 30 masu zuwa.

Laftanar Janar Oluyede ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya ke jawabi ga dakarun Operation Fansan Yamma a hedikwatar runduna ta ɗaya da ke Gusau a lokacin da ya ziyarci Jihar Zamfara jiya Alhamis.

A cewarsa, umarnin ya zama dole idan aka yi la’akari da yadda ƙasurgumin ɗan ta’addan Bello Turji ke ta’azzara hare-haren rashin imani a jihohin Zamfara da Sakkwato da kuma wasu sassan jihar Kebbi domin ganin an samu zaman lafiya a yankin.

“Ba na son jin labarin hare-haren da Bello Turji ya ke kaiwa, musamman a jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi, inda ya ke yawaita kai hare-haren ta’addanci akan al’umma. Don haka kuma na ba ku nan da kwana 30 ku yaƙi BelloTurji da muƙarrabansa a duk inda suke.”

Hakazalika Laftanar Janar Oluyede ya shaida wa sojojin cewa na Nijeriya dake ƙarƙashinsa cewar zai bada fifikon gaske wajen tabbatar da jin daɗin sojojin ƙasar baki ɗaya.

Ya bayyana cewar, tuni aka ɓullo da wani tsari na musamman na mallakar gidaje don baiwa sojoji damar mallaka kafin su yi ritaya a farashi mai rahusa a faɗin ƙasar nan.

Ya kuma ƙara da cewa, za’a samar da isassun kayan aiki da tallafi ga sojojin domin basu damar yaƙar ‘yan ta’adda da sauran ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.

A cewar shi, ziyarar tashi na da nufin yaba wa ƙoƙarin da sojojin ke yi wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar da sauran jihohin Arewa maso Yamma da kuma ƙara musu ƙarfi wajen yaƙi da ‘yan bindiga a yankin.

By ukarofi