Ɗangote da Abdulsamad da wasu sun tara biliyoyi don kafa katafaren ɗakin karatu na IBB

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Shugaban Rukunin Kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote da takwaransa na BUA, Alhaji Abdulsamad Rabi’u, sun shiga sahun masu alfarma da suka tallafa da biliyoyin kuɗaɗe domin buɗe katafaren ɗakin karatu na tsohon Shugaban mulki soja, Ibrahim Badamasi Babangida.

Ɗangote ya sanar da bada Naira biliyan 6 ne, inda ya ce zai riƙa tallafa wa aikin da Naira biliyan 2 a kowacce shekara na tsawon shekaru huɗu, haka kuma idan aikin ya wuce shekarun ba tare da an kammala ba.

Ya kuma yaba wa tsohon shugaban ƙasar a matsayinsa na wanda ya samar da tsarin masana’antu masu zaman kansu a Nijeriya, ya na mai tuna lokacin da IBB ya ba su lasisin banki su 30 a rana guda.

Haka ma Abdulsamad, wanda ya bada tallafin Naira biliyan 5 ga aikin ɗakin karatun.

Sauran sun haɗa da wanda ya samar da Gidauniyar ‘TY Ɗanjuma Foundation’, wato Theophilus Ɗanjuma, wanda ya bada biliyan N3; Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio – N50m; Arthur Eze, N500m da kuma Mustafa Chike-Obi, wanda ya bada N100m.

By Babaji