Gwamnatin Tarayya ta hana tirelolin fetur ɗaukar lita 60,000

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar tace ɗanyen man fetur ta Ƙasa, NMDPRA, ta haramta wa tireloli masu tankin da ke ɗaukar lita 60,000 na fetur hawa manyan titina a Nijeriya, wanda hakan zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Maris.

Shugaban Hukumar, Ahmad Farouk ya bayyana hakan ga manema labarai jim-kaɗan bayan kammala zaman kwamitin masu-ruwa-da-tsaki a ranar Laraba a Abuja.

Ya kuma ce, zuwa ƙarshen ɗaya bisa huɗu na shekarar 2025 babu tanka mai girman lita 45,000 da za a sake loda wa fetur.

Zaman ya ƙunshi manyan jami’ai daga hukumomin SSS, FRSC, NARTO, NUPENG, SON, DAPPMAN da kuma NMDPRA.

Ahmad Farouk, wanda Babban Daraktan tsare-tsaren rabawa da taskacewa na NMDPRA, Ogbugo Ukoha ya wakilce shi, ya ce sun ɗauki matakin ne la’akari da yawaitar hatsari tankokin fetur da ake samu akai-akai a Nijeriya.

Ya kuma yi watsi da batin da ke cewa akwai fetur mara inganci da ake raba wa gidajen mai, inda ya bayyana hakan a matsayin ƙoƙarin ruɗar da al’umma, ya na mai cewa duk fetur ɗin ake fitar wa, sai an tabbatar da ya cika ƙa’idodin tacewa kafin a yi jigilar sa ga al’umma.

By Babaji