An jinjina wa Tinubu kan bai wa ƙananan hukumomi yancin cin gashin kansu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi na ƙasa (NULGE) na ƙasa Aliyu ƙanƙara Haruna ya yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan jajircewa da yayi ya ga ƙananan hukumomi sun sami ƴancin cin gashin kansu.

Aliyu ƙanƙara yayi wannan magana ne a tattauna wa da manema labarai da yayi a garin ƙanƙara, jihar Katsina.

Ya ce babu shakka wannan mataki zai baiwa ƙananan hukumomi damar aiwatar da ayyukan raya karkara da dawo da zaman lafiya a ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro.

Shugaban NULGE yana mai tabbacin cewa nan bada jimawa matsalolin rashin abubuwan more rayuwa kamar su rashin hanyoyi masu kyau,rashin wadataccan ruwan sha, wutar lantarki da ingantaccen ilimi zai zama tarihi.

Ya kuma yabawa wasu gwamnoni da basu ciki shiga harkokin da ya shafi asusun ƙananan hukumomi.

Haruna ƙanƙara ya yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa kulawar da yake baiwa ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar.

Ya kuma yabawa gwamnan kan samun nasarar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.

Shugaban ya bada tabbacin cewa NULGE zata yi bakin ƙoƙarin ta, wajen ɗaukaka daraja da walwalan ya’yan ƙungiyar.

Aliyu ƙanƙara ya riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar ya riƙe muƙamin shugaban har karo na biyu a jihar Katsina,ya kuma riƙe muƙamin ma’ajin kuɗi ƙungiyar ta ƙasa kafin zama shugaban ta na ƙasa baki ɗaya.

A wannan wata mai zuwa zai kama aikin ƙungiyar.

By ukarofi