Daga AISHA ASAS
Fitaccen mawaƙi Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani Portable, ya yi iƙirarin cewa, ba ya cikin mutane masu lafiyyyar ƙwaƙwalwa, inda ya kira kansa a matsayin ‘mahaukaci’. Sannan ya bayyana cewa, yanzu haka yana karɓar magani a asibitin ƙwaƙwalwa ta Gwamantin Tarayya da ke Aro, da ke cikin Abeokuta, wato Federal Neuropsychiatric Hospital, Aro.
Mawaƙi Portable ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya saki a ranar Talatar da ta gaba, wanda ya yi shi cikin harshen Yarbanci, tare da surki da Ingilishi.
Mawaƙin wanda ya yi ƙaurin suna a aikata ayyukan da ba su dace ba, ya roƙi gwamnatin JIhar Ogun da ma al’ummar Nijeriya bakiɗaya da su yi masa uzuri, kuma su dubi matsalar hauka da yake tare da ita, kafin su yi masa hisabi kan abinda ake tuhumarsa da aikatawa.
An zargi mawaƙin da kitsawa tare da jagorantar harin da aka kai wa wasu ma’aikata daga Ma’aikatar Tsare-Tsare da Raya Birane ta Jiha.
Lamarin wanda ya faru ne a gidan giya na Odogwu da ke Oke-Osa, Tigbo Ilu Ota, inda ma’aikatan suka nemi shadar tsarin ginin wanda aka amince da ita a hukumance. Wanda suka nema daga wurin mahaifin Portable, kasancewar yana wurin a lokacin.
Da wannan ne rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta bayyana cewa, tana neman fitaccen mawaƙi Portable, kan zargin abinda suka kira da mummunan harin da aka kai wa ma’aikantan Ma’aikatar Tsare-Tsare da Raya Birane ta Jihar Ogun.
A cewar rundunar ta ‘yan sanda, mawaƙi Portable ɗauke da makami ne ya jagoranci wasu gungun ‘yan daba guda tara ɗauke da muggan makamai wajan far wa jami’an, waɗanda aka tabbatar ba su ɗauke da kowane irin makami.
Wannan hari ya yi sanadin raunana jami’an, wanda suka sha da ƙyar, bayan nasarar tserewa da suka samu ne suka kai rahoton faruwar lamarin a rundunar ‘yan sanda ta yankin Ota.
Mawaƙi Habeeb dai ya sha samun kansa a rigima kala-kala, ƙarama da babba wadda ta kai har a tsakanin su mawaƙa bai cika tagomashi ba. Yayin da waɗansu ke masa kallon ɓara gurbi a tsakanin mawaƙa.
Za mu iya cewa ba a iya mawaƙa ba, Portable ya kasance mawaƙin da dayawan mutane suka sallama shi ga mutanen banza daga cikinsu, inda suke ganin ba wanda zai so mawaƙin sai mai hali irin nasa.
Duk da cewa, a kwanankin baya ya samu murmushin mutane da dama, yayin da suka nuna soyayya gare shi, ba kuwa komai ya kawo hakan ba face nuna yatsa da suka fara da fitaccen ɗan daudu Idris, wanda aka fi sani da Bobrisky, a daidai lokacin da jama’a suka cika zuciyarsu da ƙiyayyarsa, wanda hakan ya sanya waƙar da mawaƙi Portable ya fitar musamman don ɗan daudun mai taken ‘Brotherhood’ ta samu karɓuwar jama’a duk da cewa ba wani daɗin azo a gani ta yi ba.
