Tsakanin Emefiele da DSS

Spread the love

Babban bankin Nijeriya ya sanar da dawowar gwamnan bankin Godwin Emefiele daga hutu a ranar Litinin bayan wasu jita-jita da aka yaɗa sun ce yana ta gudu domin kada hukumar DSS ta kama shi.

A wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar, daraktan watsa labarai na bankin Osita Nwanisobi ya bayyana cewa, “gwamnan ya dawo domin ci gaba da aiki da ƙarfinsa kafin taron farko kwamitin tsare-tsare na bankin da za a gudanar a ranakun 23 da 24 ga watan Janairun 2023.”

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a shirye Emefiele yake ya ci gaba da bin dokokin ƙasar da kuma umarnin Shugaban Nijeriyar Muhammadu Buhari.

A ɗayan ɓangaren kuma hukumar tsaro ta DSS ta fitar da sanarwa inda ta ce jami’anta ba su kai samame Babban Bankin Nijeriya CBN ba haka kuma ba su kama shugaban bankin ba.

An fara samun rahotannin yunƙurin kama Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Nijeriya da ‘yan sandan farin kaya ta DSS suke son yi ne a watan Disamban 2022.

Wannan ya biyo bayan watsi da buƙatar kama Emefiele ne da wata babbar kotu a Abuja ta yi da DSS suke son yi.

Wani mutum ne mai suna Gambarawa ya shigar da ƙara a madadin DSS a ranar 7 ga watan Disamban 2022.

Hukumar tsaro ta DSS ɗin ta zargi gwamnan babban bankin da cewa yana taimaka wa ayyukan ta’addanci saboda ya aikata laifi da ya shafi tattalin arziki.

Mai shari’a John Terhemba wanda ya jagoranci zaman ne ya kori ƙarar da aka shigar.

Ya ce, DSS ba su gabatar da ƙwararan hujjoji ba da za su nuna gwamnan na da hannu a taimaka wa ta’addanci da aikata laifuka da suka shafi tattalin arzikin ƙasa.

Tun bayan da babban bankin Nijeriya ya sanar cewa za a fara amfani da wani sabon tsari wanda ya haifar da samar da sabbin takardun Naira, gwamnan CBN ke ta fuskantar matsin lamba.

Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa saboda damuwar da ta nuna kan sabon tsarin, hakan ya zo ne bayan da Ministar Kuɗi ta Nijeriya, Zainab Ahmed ta ce ba ta da labarin sabuwar dokar.

Haka kuma, Majalisar Wakilai ta gayyaci gwamnan domin ya amsa tambayoyi kan sabbin takardun Naira da za a fara amfani da su da kuma yadda za su shafi tattalin arziki.

Wasu lauyoyi masu rajin kare haƙƙin bil adama da mambobin jam’iyyun adawa da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu sun fara zanga-zanga a kan tituna domin adawa da matsin lambar da Emefiele ke fuskanta.

Masu zanga-zangar ƙarƙashin haɗakar ƙungiyar masu kare muraddun ƙasa ta CNID sun ce hukumar tsaro ta farin kayan, DSS ta shigar da ƙarar ne don neman a binciki gwamnan kan zargin taimaka wa ta’addanci.

Haɗakar ta yi kira ga Shugaba Buhari da Atoni janar na Nijeriya, Abubakar Malami da su saka baki cikin lamarin.

Wasiƙa daga AMINU YAA, 08062327373. 

By ukarofi