Pafaroma ya na mawuyacin hali, inji fadar Vatican

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Fadar Vatican ta bayyana cewa, Pope Francis (Pafaroma), yana fama da matsalar cutar numfashi, wato ‘Asthmatic Respiratory Crisis’ na tsawon lokaci wadda ke buƙatar agajin adadin numfashi mai yawa.

Pafaroma mai shekaru 88, an kwantar da shi ne a asibiti na tsawon mako guda sakamakon cutar sanyi ta ƙoda da ke damunsa, wadda likitoci suka ayyana ta a matsayin nimoniya.

Sanarwar da Vatican ta fitar ta ce, bayan wasu gwaje-gwaje da aka yi masa, an kuma ƙara masa jini ganin cewa hakan na da alaƙa da cutar anemiya.

Likitoci sun tabbatar da cewa za a ƙara masa wa’adin sati ɗaya la’akari da halin da ya ke ciki.

Duk da cewa jagoran kiristocin ba ya fadar, an cigaba da gudanar da bukukuwan shekara mai alfarma a ranar Asabar.

By Babaji