
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) na shan suka daga ƴan Nijeriya, biyo bayan shaidar da ya bayar a littafinsa ta soke zaɓen ‘June 12, 1993’.
Ƴan Nijeriya da suka rayu a zamaninsa da waɗanda suka zo a bayansu sun yi watsi da bayanan da ya bayar, tare da bayyana su a matsayin ƙoƙarin sake rubuta tarihi da guje wa ɗaukar laifi.
A sabon littafin IBB mai suna ‘A journey in Service’, ya tabbatar da cewa ɗan takarar jam’iyyar SDP, wato Marigayi Moshood Abiola shi ne sahihin wanda ya lashe zaɓen.
IBB ya ce, babu tantama kan cewa Abiola, wanda aka fi sani MKO Abiola shi ne ya lashe zaɓen ‘June 12’, ya na mai bayyana cewa kuri’a 8,128,720 ya samu, wanda hakan ya ba shi damar doke takwaransa, wato Bashir Tofa da ya samu ƙuri’a 5,848,247.
Babangida ya ɗora laifi ga sojoji ƙarƙarshin jagorancin Marigayi Janar Sani Abacha, ganin yadda hakan ya sababa zanga-zanga da tashin-tashina na tsawon lokaci kafin dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999.
IBB ya ƙara da cewa, a ranar 23 ga watan Yuni, 1993 ya je Katsina ta’aziyyar rasuwar Marigayi Musa Yar’adua, wato mahaifin tsohon Shugaban ƙasa, Marigayi Umaru Musa Yar’adua, wanda shi ne lokaci na farko da aka sanar da soke zaɓen ba tare da an sanar da shi ba, kamar yadda ya faɗa.
Duk da waɗannan bayanai da IBB ya yi, tarihi ya nuna yadda aka gan shi a wani gidan talabijin don ya sanar da batun soke zaɓen, wanda daga bisani a watan Agustan shekarar ya shelanta yin murabus.
Daga nan ya ɗora Ernest Shonekan a matsayin Shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya, inda a watan Nuwamba ne Abacha ya karɓe mulkin daga hannunsa.
Tsohon shugaban Hukumar Ƴancin Ɗan-adam kuma Lauya, Chidi Odinkalu, ya soki IBB kan jingina maganganu akan waɗanda ba za su iya kare kawunansu, ya na mai cewa littafin nasa a cike ya ke da zarge-zarge akan matattun mutane.
Daga cikin suaran waɗanda soki kalaman tsohon shugaban ƙasar akwai ƴar Abacha,wato Gumsu Sani Abacha, wadda ta wallafa kalamai kamar haka a shafinta na X; “Allah baya bacci fa!! Muyi hattara da duniya wallahi.”
