
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon shugaban mulkin Soja na Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ce an kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari ne saboda rashin gamsuwa da salon mulki da tsare-tsarensa a 1985.
IBB shi ne shugaban mai’aikatan gwamnatin Buhari a wancan lokaci, bayan juyin mulkin da Buhari ya yi wa Shugaban mulkin farar hula, Marigayi Shehu Shagari a ranar 31 ga watan Disambar 1983.
A cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’, IBB ya ce gwamnatin Buhari ta yi amfani da dokoki masu tsauri waɗanda suka kai ga tauye haƙƙin ɗan-adam da ƴancin ƴan ƙasa.
Ya ƙara da cewa, juyin mulkin da ya kai Buhari hawa kujerar shugabancin ya yi sanadiyyar samuwar rarrabuwar kai acikin sojoji, wanda kuma hakan abu da ya yi tasiri matuƙa ga goben al’ummar Nijeriya.
IBB ya bayyana mulkin Buhari a matsayin hanyar tsawwala wa ƴan Nijeriya, ya na mai cewa a saboda haka ne suka ɗauki matakin kifar da gwamnatin don dawo da kyawawan zato da martabar ƴan ƙasa.
