DAGA COMRADE IBRAHIM ABDU ZANGO
Tun lokacin da aka ƙirƙiri salon dimukraɗiyya a ƙasar Amurka, wato ƙasar “Yankee” suka ɗauka cewa sune duniya. A taƙaice dai tun yaƙin duniya na biyu Amurka take taka rawar ita ce ƙasa mafi ƙarfin ababe guda biyu na soji da kuma ƙarfin tattalin arziƙi! Waɗannan abubuwa guda biyu sune ya sa a yau duk shugaban Amurka yake cewa “America First”, wato babu wani abu cikin zuciyarsa, sai Amurka kawai, ita ce alƙiblarsa kuma ita kawai yake bautawa! Ita wannan niyya akanta yake kuma zai iya bayar da ransa bisa burin ɗaukakar Amurka. Duk shugaban Amurka ya kan cewa lokacin neman kujera cewa Amurka ce da farko kafin komai a rayuwarsa.
Tun daga George Washington zuwa Abraham Lincoln har J. F. Kennedy, George Bush babba da George Bush ƙarami zuwa Niɗon, Johnson da Bill Clinton har mugu Biden, wato Joe Biden, da wanda yake kiran kansa “crazy”, wato Donald Trump; dukkansu “America First” shine takensu. Duk da wannan take, Amurka da shugabanninta ba sa buƙatar wani ya ɗauki wannan salo domin kishin ƙasarsa, kususan ƙasashe masu tasowa, domin duk wanda ya ce shi ƙasarsa kawai sai sun ga bayansa, wannan kuwa ba wai a Afrika ba a’a har ƙasashen Larabawa waɗanda ba su shafi Nahiyar Afrika ba. Kowa ya san yadda suka ragargaza Iraƙi, yanzu kuma Siriya, inka dawo Afrika ta Arewa sai kuma Libya, waɗannan ƙasashe biyu na Larabawa su ma sun ƙudiri cewa ƙasarsu ce farko, kafin komai! Me ya faru? Yaƙarsu aka yi sai da aka ga bayansu, domin kawai sun rungumi girman ƙasashensu kamar yadda Amurka take buƙatar shugabanninta su yi mata. Yau maganar Shariff Saddam da ɗau uwansa Mu’ammar Ghaddafi sai kawai mu yi addu’a Allah Ya jiƙan bayinsa masu son ɗaukakar ƙasashensu, kuma suka gamu da sharrin turawan yamma da kisisinar Yahudu tuba babu, Allah Ya tsare mu, Amin.
Yaya ababen suke idan aka dawo ƙasarmu ta haihuwa Nijeriya? Na san dai da cewa, mu ma mun yi shugabanni na soji da farar hula, amma na farar hula sune alkiblarmu domin sune suka karɓi mulki daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960, kuma shugabannin nan mutane ne masu kamala da tsoron Allah, ina magana ne akan su Sir Abubakar Tafawa Balewa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, dukkansu biyun ‘Yan Arewa ne na gidi masu ƙaunar Nijeriya cikakkiyar ƙauna; dukkansu musulmi ne, basu nuna banbancin addini ko ƙabila. Allah cikin ikonsa sai ya kasance sun ce Nijeriya ce farko, wato ƙaunar ƙasa itace niyyarsu, amma saida maƙiya Nijeriya ciki da waje suka kawo ƙarshen mulkin waɗannan Waliyyan Allah, saboda idan aka kirasu da Waliyyai dai-dai ne, saboda sun nuna tsoron Allah bisa mulkinsa, kuma sun koma ga Allah cikin nutsuwa domin kisan gilla akayi musu, domin wasu “‘Yan Bado” ne sukayi musu juyin mulki, wanda sun yi yadda suke so, kuma Allah Ya komar musu da sharrin ababen da suka aikata. Wai don me zasu ga Nijeriya farko a zuciyarsu “Nigeria First”? To bayan waɗannan bayin Allah an sami juyin juya hali na soja fiye da kima, kuma a sukansu jamhuriyoyin biyu sun taka rawa sosai “Nigeria First”, wato na farko marigayi Janar Murtala da na biyu marigayi Janar Sani Abacha: waɗannan biyu kowa yaga rawar da suka taka ta “Nigeria First” kuma anga yadda ta kaya; shi Janar Murtala da rana tsaka aka kai masa hari wato kenan ranar Juma’a zai tafi Masallaci aka kai masa hari, domin kawai ya tsaya da ƙafarsa domin kyautatawa Nijeriya da ‘ya’yanta, shima ya bada ransa domin ‘yan Nijeriya sa rayu.
Haka Janar Sani Abacha shima dai sammakal, inji ɗanbarno, ni magana ga ‘yan Nijeriya ita ce wai domin mene ne idan shugaba yazo kyautata wa Nijeriya ‘yan kore suke cusa mana ƙiyayyar duk wanda yazo tsara mana kishin ƙasa da tanada mata mafita? Sau da yawa na ga shugabanni irinsu Marigayi Umaru Musa Yar’Adua da Alhaji Shehu Shagari dukkanninsu ‘yan Arewa ne, sun zo da ƙudire-ƙudire masu kyau, domin kyautata wa Nijeriya, amma yaya ta kaya? Alhaji Shehu Aliyu Shagari yayi baƙin jinni ne, domin yaƙi yarda da tsarin Amurka na karɓar wani abu wai shi “SAP” Turancin da ‘yan Ingila suka ce ba su tantance da shi ba, wato “Structural Adjustment Policy”, wanda niyya ce ta lalata dukkan hanyoyin rayuwa ta talakawan ƙasa. Babu wata ƙasa a turai data taɓa karbar wannan muguwar hanya wacce za’ace gwamnati ta ɗauke komai ana jin daɗin talakawa kuma su shugabanni suna cikin “lagwada” Wal’iyazu Billahi.
Alhaji Shehu Shagari, Allah Ya jiƙan sa, ya ƙi karɓar wannan tsari, shine dalilin da ya sa aka yi masa abinda ya faru a gareshi, shiko marigayi Umaru Musa Yar’adua wanda ya bashi mulki shine ya tsara masa abubuwan ashsha, shi kuma yace “Wayo Yasan Naƙi” ya ture dukkan wani bigire, wannan shine ya haifar mana da abinda ake zargin ya kawo mana alkaba’in Boko Haram bisa zargi; shugaba Umar Musa Yar’dua ya kawo canje-canje da zasu kyautatawa talakawan Nijeriya domin ya yarda da “Nigeria First”. Amma duk niyyarsa saida wasu ‘yan siyasa suka biya ta Janar Obasanjo, kuma ‘yan Arewa suka nuna ƙiyayyarsu ƙiri-ƙiri ga aniyar marigayi Umaru Musa Yar’adua ta kyautatawa talakawan Nijeriya. Kaga dai yadda Janar Obasanjo ya nuna aniyarsa ta sai ya zarce wanda ta wannan niyya ce har ya komar da zaɓen ƙananan hukumomi ya koma na jihohi, sannan kuɗaɗen ƙananan hukumomi suka koma hannun gwamnonin jihohinsu, wannan dukka anyi haka ne domin sharewa Obasanjo hanyar tazarce, wannan ko shakka babu dalilin haka ne ya tsara yadda shugaba Umaru Musa Yar’adua sharri shi kuma ya farga yaƙi aiwatarwa, wanda wasu daga cikin yaran Obasanjo a cikin gwamnoni suka riƙa yiwa marigayi tutsu da buga hotonsa da kan jaki!
Oho, shine hanyar da shugaba Buhari ya biyo ta shiryawa shugana Ahmad Bola Tinubu wacce yanzu ya zama abin aibatawa, kususan da Yan’uwa ‘yan Nijeriya bamu gane ba cire tallafin man fetur da ɓoye kananzir mutane ba sa ganin sa, da son canjin kuɗin Nijeriya da jinginar da tashoshin girjin sama na Kano da Abuja; kai ababen fa akwai takaici bisa tsuntsun tsaru tsuhu wato tsun-tsun tsura tsuhu: Gaskiya malam Shugaba Tinubu lallai ka gyara dawo da ‘airports’ ɗin Kano da Abuja sannan binciki ko’ina.
Naku; Comrade Ibrahim Abdu Zango
Shugaban Kano Unity Forum,
No. 260, Zango Quarters, Kano, Jihar Kano – Nijeriya
21 ga Janairu, 2025
