Buhari da El-Rufa’i da Amaechi sun ƙaurace wa taron jagororin APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jagororin APC a mataki na ƙasa sun taru a Sakatariyar jami’yyar dake Abuja domin gudanar da taron kwamitin majalisar zartarwa (NEC).

Jami’an tsaro sun cike hanyoyin dake kai wa zuwa ga sakatariyar waɗanda suka haɗa da sojoji da jami’an Guards Brigade, inda aka taƙaici zirga-zirgar ababen hawa da na mutane.

Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron da wuri sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari da Ministan Kasafi, Atiku Bagudu da Mataimakan Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.

Sauran sun haɗa da Gwamnonin Jihohin Edo, Benue, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Neja, Legas, Kogi, Ogun da kuma Imo.

Haka kuma, akwai mataimakin gwamnan Ebonyi da tsofaffin gwamnonin jihohin Kogi, Neja, Filato, Kebbi da Zamfara.

Har’ilayau, Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Umar Ganduje da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas su ma sun halarci taron.

By Babaji