Sarkin Musulmi ya bada umarnin duba jinjirin watan Ramadan yau

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa ranar Juma’a 28 ga Fabrairu, 2025 za a fara neman jinjirin watan Ramadan 1446AH.

A cewar wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, Farfesa Sambo Wali Junaidu, an umurci Musulmi da su duba jinjirin watan tare da kai rahoto ga Hakiminsu ko ƙauye mafi kusa.

Daga nan za a sanar da Sarkin Musulmi da kuma Shugaban Majalisar ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya Muhammad Sa’ad Abubakar, don bayar da sanarwar a hukumance.

By ukarofi