Gwamnatin Tarayya ta rufe gidajen man Total, Ashafa da wasu uku saboda ɓoye mai a Katsina

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) reshen Jihar Katsina, ta rufe gidajen mai guda biyar bisa laifin ɓoye mai.

Aikin, ƙarƙashin jagorancin kwanturola na jihar, Umar Muhammad, an yi shi ne don tabbatar da bin ƙa’idojin harkar mai da kuma kare haƙƙin masu sayayya.

Gidajen mai guda biyar da abin ya shafa sun haɗa da Total, A.A. Rano, Ashafa, Maje Gas da Gwagware.

An tattaro cewa, aikin tabbatar da bin dokar ya maida hankali ne kan gidajen mai da lasisin aikin su ya ƙare kuma sun ƙasa sabunta lasisin kamar yadda hukumomi suka buƙata.

Yawancin gidajen man da abin ya shafa kuma an rufe su ne saboda yadda suke gudanar da harkokin samar da man fetur, da harkokin abokan ciniki.

Hukumar ta gargaɗi gidajen man fetur da su karkata akalar man da aka ware musu, inda ta bayyana cewa duk gidan man da aka samu da laifi za a yi maganinsa, kamar yadda aka gindaya sharuɗɗa.

Muhammad ya nanata ƙudurin hukumar na tabbatar da tsaro da gaskiya a ɓangaren man fetur, yana mai jaddada cewa za a gudanar da irin wannan ayyuka a faɗin jihar domin kiyaye ƙa’idoji da kuma kiyaye buƙatun masu amfani.

By ukarofi