Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A wani yunƙurin gwamnatin shugaba Tinubu na bunƙasa tattalin arziki ta hanyar kasuwancin abincin Halal Nijeriya ta rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya da Kamfanin Bunƙasa Kayayyakin Halal na ƙasar Saudi Arabiya, wannan yarjejeniyar za ta bai wa Nijeriya damar shiga jerin ƙasashen duniya da za su ci ribar da ta kai kimanin dalar Amurka har tiriliyan 7.7 a kasuwar halal ta duniya.
Bugu da ƙari, wannan haɗin gwiwar zai tabbatar da Nijeriya a cikin jagororin bunƙasa tattalin arzikin halal, tare da samar da ayyukan yi, da kuma janyo hankalin masu saka hannayen jari daga ƙasashen waje.
Kazalika yarjejeniyar za ta sauƙaƙe hanyoyin saka jari, da musayar bayanai da ilmin fasaha, da buɗe damammakin hada-hadar kasuwanci a cikin mahimman sassan ciki da wajen Nijeriya, gami da samar da abinci, da magunguna, da bunƙasa kiwon dabbobi.
A yayin rattaba Hannun, mai wakiltar Mataimakin Shugaban ƙasa, kuma Mataimakin shugaban ma’aikatar fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hasan Hadejia, ya bayyana wannan yarjejeniyar a matsayin wata Damar Allura a cikin ruwa da Nijeriya ta yi rabon tsintowa, inda ya ce daga yanzu Nijeriya ta shiga jerin ƙasashen duniya da za su bigi ƙirji wajen cin gajiyar kasuwancin da ‘yan ƙasar za su yi naam da ita.
