
Daga BELLO A. BABAJI
Dakta Mariya Mahmoud, wadda ita ce ƙaramar Ministar Abuja, ta ce jam’iyyar APC na shirin lashe duka kujerun ƙananan hukumomin babbar birnin, wanda za a yi a watan Fabrairun 2026.
Ministar ta bayyana hakan ne a yayin taron masu-ruwa-da-tsaki na APC da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis.
Ta kuma ce, kamar haka suke fatan samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027.
Ta ce, sun gano matsalolin jam’iyyar tare ɗaukar matakan warware su da fuskantar zaɓen.
Haka kuma, ta ƙara da cewa, za su tabbatar da cewa ba a bi son ran wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyyar ba, inda ta ce za a mayar da hankali ne akan abin ya dace da zai kai su ga nasara.
Kazalika, Dakta Mahmoud ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samar da tsarin damawa da mata da matasa ta hanyar samar da sakatariya ga kowane ɓangare.
Shugaban jam’iyyar na Abuja, Abdulmalik Usman ya yaba wa jagororinta ganin yadda suka tsaya wajen ɗinke ɓarakar da ke cikinta.
