Rundunar Sojojin ƙasa ta ninka wa dakaru kuɗin alawus na abinci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Sojojin ƙasa, Laftanal Kanal Olufemi Oluyede ya sanar da ƙari a kuɗin abinci ga jami’ansu, wanda daga N1,500 ya koma N3,000 a kullum.

Daga ƙarshen watan Maris ne za a ƙaddamar da ƙarin ga dakarun.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga jami’an runduna ta 81 a Filin Faretin Birget na 9 dake Ikeja a Jihar Legas.

Shugaban sojojin ya koka ga yadda ake bai wa jami’an N1,500 a matsayin kuɗin abinci na kowacce rana, ya na mai tabbatar masu da ƙoƙarinsa na inganta walwalarsu.

Ya kuma ce, yana sane da irin ƙalubalen wajen zama da suke fuskanta musamman waɗanda ba su da gidaje bayan sun yi ritaya.

Game da hakan ne ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin samar da gidaje ga jami’an da suka yi ritaya.

By Babaji