Ƙara farashin kira zai sa a samu ingancin sabis – Minista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani, Dakta Bosun Tijani ya ce ƙarin kaso 50 da kamfanonin Telekom suka yi zai taimaka wajen samun ingantaccen sabis ga ƴan Nijeriya.

Ministan ya bayyana haka ne wa manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa, ranar Alhamis.

Ministan ya jagoranci tawagar kamfanin Bharti Airtel ƙarƙashin jagorancin Shugabansa, Sunil Mittal a wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Dakta Bosun ya ce, hukuncin karin farashin ya zama dole ganin yadda gwamnati take ƙoƙarin samar da maslaha a tsakanin al’umma da kamfanonin.

Ya ƙara da cewa, gwamnati ta amince da ƙarin farashin ne don guje wa rasa ayukka da fargabar ficewar wasu kamfanoni daga Nijeriya.

Hakan kuma, Ministan ya ce Nijeriya ta zuba jari a samar da kilomita 90,000 na sinadarin ‘fiber’ da zai wadaci baki ɗaya sassan Nijeriya.

Har’ilayau, Gwamnatin Tarayya ta amince da samar da turakun telekoms guda 7,000 a ƙauyukan Nijeriya don samun wadataccen sabis ga al’umma.

By Babaji