Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Hafsan Sojin Sama na Nijeriya Air Marshall Hassan Abubakar ya ce ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga ƙungiyar Ecowas ta ƙara ɗora wa rundunar sojin Nijeriya nauyi.
Ficewar ƙasashen na Alliance of Sahel States (AES) daga tsarin aiwatar da tsaro ya birkita alƙiblar tsarin gaba ɗaya, a cewarsa yayin da yake magana yayin wani taron kwamandojin sojin sama a Abuja ranar Laraba.
Ya ƙara da cewa hakan zai shafi rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) kai-tsaye, wadda ke yaƙar ƙungiyoyin Boko Haram da Iswap a Nijeriya, da Nijar, da Chadi, da Kamaru.
“Matakin da suka ɗauka na fita [daga Ecowas], da kuma Chadi da ke tunanin ficewa, zai shafi ikon MNJTF na gudanar da ayyukanta,” kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito shi yana faɗa.
“Saboda haka nauyin da ke kan rundunar sojin Nijeriya domin tallafa wa MNJTF zai ƙaru, wanda zai buƙaci cikakken martani da tsari daga rundunar sojin sama ta Nijeriya.
