Yadda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da maijego da mutane 37 a Kaduna duk da yin sulhu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan binda sun yi garkuwa da Wakilin Fulani na ƙauyen Janjala Alhaji Atah Adamu Wakili, wata maijego da mutum 37 dake ƙaramar Hukumar Kagarko a jihar Kaduna duk da iƙirarin sulhu da aka yi da su kwanakin baya a jihar.

Maharan sun afka ƙauyen da ƙarfe 10 na daren Lahadi inda suka tafi da shanu daga wata ruga dake kusa da ƙauyen.

Wani basarake a ƙauyen ya sanar da haka ranar Litini yana mai cewa maharan sanye da kayan sojoji ɗauke da muggan makamai sun riƙa bin mutane gida-gida suna garkuwa da su.

“Na samu labarin abin da ya faru da ƙarfe 10 na dare inda nake jin cewa maharan sun yi awon gaba da Wakilin Fulanin Janjala, matansa da babban ɗansa Abubakar mai shekarar 37.

“Jami’an tsaron daga Kagarko sun iso ƙauyen da ƙarfe 11 na dare inda a lokacin maharan duk sun tafi da dabobbi da mutanen da suka yi garkuwa da su daga ƙauyen.

“Wannan harin ya faru bayan makonni da wasu maharan suka kai wa ƙauyukan Mai-Iddo, Gidan Maƙeri da Kuchimi hari ranar 11 ga Fabrairu inda suka yi garkuwa da matar fasto da mutum 15.

“Maharan sun ƙona gidaje da rumbunar abincin mazauna ƙauyen.

“Zuwa yanzu maharan na buƙatar a biya naira miliyan 50 da babura shida kafin su sako mutanen.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da garkuwa da mutanen da aka yi a ƙaramar hukumar Kagarko sai dai bata ce komai ba.

By ukarofi