Shugaban MOPPAN ya yi wa al’ummar Musulmi barka da zuwan Ramadan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban ƙungiyar ƴan fim ta Ƙasa (MOPPAN), Umar Mai-Kuɗi ya aika da saƙon barka da shigowa watan Ramadan ga al’ummar Musulmi.

Ya ce, yayin da suka shaida farkon watan, ya na mai fatan hakan ya zama sanadin ƙara kusancinsu ga Allah (SWT).

Ya yi masu fatan samun rahamarSa da kariyarSa a yayin da suke azumi da sauran ibadu a acikinsa.

Haka kuma ya yi fatan addu’o’i da azumi gami da kyawawan ayyukansu su zamo karɓaɓɓu.

Kazalika, Mai-Kuɗi ya yi fatan abadunsu su zamo sanadin yafe masu kurakuransu, tare da fatan alkhairi ga kowane musulmi.

By Babaji