Daga USMAN KAROFI
Fiye da ‘yan Najeriya 20,197 da suka maƙale a ƙasashe daban-daban sun dawo gida.
Bayanan da aka tattara daga shirye-shiryen mayar da su gida da hukumar kula da hijira ta duniya (IOM) ta gudanar, tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashen waje, sun tabbatar da hakan.
Mata da ‘yan mata sun kai kusan kashi 88 cikin 100 na waɗanda aka dawo da su, yayin da maza suka kai kashi 13.
A cewar rahoton, mafi yawan waɗanda suka maƙale sun dawo ne daga ƙasashen da ke kan hanyoyin bakin haure na Mediterranean, ciki har da Libya da Italiya.
Tun daga Afrilu 2017 zuwa Mayu 2018, fiye da mutum 7,000 aka dawo da su daga gidajen ajiye baƙin haure da kuma biranen Libya, yayin da wasu 750 suka dawo daga ƙasashen maƙwabta kamar Nijar da Mali.
Hukumar IOM ta bayyana cewa daga Afrilu 2017 zuwa Fabrairu 2022, jimillar ‘yan Najeriya 19,452 aka taimaka musu don komawa gida cikin yardarsu.
A farkon watannin 2024 kaɗai, hukumar ta mayar da mutum 167 gida, inda kashi 81 cikin 100 daga cikinsu mata ne.
Rahoton ya kuma bayyana cewa dalilin da ya fi haddasa wannan hijira ta ba bisa ƙa’ida ba shi ne matsalar tattalin arziki, inda kashi 94 cikin 100 na waɗanda aka dawo da su suka ce suna neman kyakkyawar rayuwa ce.
Libya ta kasance ƙasa mai yawan cin zarafi ga baƙin haure daga Najeriya, inda aka yi amfani da su a matsayin bayin aiki da kuma cin zarafin mata. Mali kuwa ta fi shahara wajen sayar da mata domin karuwanci, inda fiye da mutum 1,109 aka ce an tilasta su yin hakan, mafi yawansu mata ne.
Hukumar IOM tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi na gwamnati da na ƙwararru suna ba wa waɗanda suka koma gida tallafin sake farfaɗowa, ciki har da kula da lafiyarsu da kuma koyar da su sana’o’i don dogaro da kansu.
