Tsohon ɗan wasan Arsenal, Ozil ya shiga siyasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon tauraron kwallon kafa, Mesut Ozil, ya shiga harkar siyasa a Turkiyya bayan da ya samu kujera a babban kwamitin jam’iyya mai mulki ta ƙasar.

An zaɓi Ozil ne a yayin babban taron jam’iyyar a birnin Ankara a ranar Asabar, wanda hakan ke ƙara nuna karfin alaƙar da ke tsakanin sa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Ozil mai shekaru 36, ya samu ƙarin kusanci da Erdogan ne a shekarar 2019, a lokacin da ya auri tsohuwar wacce ta fi kowa kyau a Turkiyya, Amine Gulse, wanda hakan ya zama ɗaya daga cikin dalilansa na shiga siyasa.

Tsohon ɗan wasan na tsakiya, abin kwaikwayo ne a lokacin da ya ke buga ƙwallon ƙafa, inda ya buga wa ƙasar Jamus wasannin 92 da lashe Kofin Duniya a shekarar 2014.

Haka kuma ya zama gwarzon ɗan wasan shekara na Jamus har sau biyar a lokacinsa.

Saidai, wa’adinsa da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jamus ya zo ƙarshe ne a shekarar 2018 bayan gasar Kofin Duniya, lokacin da ya zargi gidajen jaridun ƙasar da hukumar ƙwallon ƙafarta da nuna wariyar launin fata, biyo bayan suka da ya sha daga ƴan ƙasar kan yin hoto da Shugaba Erdogan da ɗan wasa Ilkay Gundogan.

Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Jamus, Reinhard Grindel ya zargi Ozil da cewa ana amfani da shi domin cimma manufar siyasa.

Amma ɗan wasan ya musanta zargin da cewa ya yi hakan ne don nuna girmamawa ga ƙasar mahaifansa.

A shekarun baya ne Ozil ya riƙa sukar tauye ƴancin ɗan-adam da rikici da ke faruwa a sassa daban-daban na faɗin duniya, inda aka samu yana sukar Chana bisa musguna wa musulman yankin Uyghur dake ƙasar.

Lamarin da ya sabbaba tsohuwar ƙungiyarsa, wato Arsenal ta barranta daga kalaman ɗan wasan.

Bugu da ƙari, Ozil ya tsoma baki a rikicin Nagorno-Karabakh da ke tsakanin ƙasar Armeniya da Azerbaijan, da kuma na nuna goyon bayansa ga ƴancin Palastinawa da alla-wadai da ayyukan Isra’ila.

By Babaji