Boko Haram sun yi garkuwa da farfesa da fasinjoji a hanyar Damaturu zuwa Biu, sun kashe wasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu ƴan ta’adda da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram/ISWAP ne, sun sace Farfesa Abubakar El-Juma na Jami’ar Sojoji ta Biu (NAUB) tare da wasu fasinjoji.

Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi a yankin ƙauyen Kamuya, wanda ke da nisan kilomita 10 tsakanin sa da Buratai, garin tsohon shugaban Sojojin ƙasa, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya).

El-Juma shine Shugaban Tsangayar nazarin Injiniyanci, wanda kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran ba su muƙamin shugaban jami’ar.

Rahotanni da dama sun tabbatar da cewa irin haka ya sha faruwa a hanyar, wadda ake yawan yin garkuwa da mutane da dasa boma-bomai a tsawon shekaru 10.

Wata majiya ta jami’an tsaro ta ce, an sace matafiya da ba a san adadinsu ba a wasu motoci ƙirar Golf guda biyu da wata ta Borno Express a hanyar.

Majiyar ta kuma ce, mayaƙan sun ƙyale fasinjoji mata su yi tafiyarsu, yayin da suka yi garkuwa da sauran mazan, ta na mai riƙon al’umma da ta sanya su acikin addu’o’i albarkacin watan Ramadan.

A wani labarin kuma, mayaƙan Boko Haram na ɓangaren Mallam Sadiƙu, sun kashe wasu mutane 11 a wani hari da taskar dare a wata mahaƙar gwala-gwalai a ƙauyen Karaga dake kusa da maɓoyar ƴan ta’addar, a ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Lamarin ya auku ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, wanda muryoyi daga ƴan gari da jami’an tsaro suka tabbatar da cewa waɗanda aka kashe mutane ne da ke aikin haƙar ma’adanai daga garin Bassa da ƙauyukan da suke kewaye da shi.

Bassa gari ne da ya fuskanci ƙalubale na hare-haren ƴan Boko Haram, waɗanda suka yi sanadiyyar ɗaiɗaita garin da al’ummarsa.

By Babaji