
Daga BELLO A. BABAJI
Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta umarci kwamitin bincike akan ƙwarewar aiki na Majalisar Dattawa da ya dakata da shirinsa na gudanar da bincike akan kalaman Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Alƙali Obiora Egwuatu ya bada umarnin a wata takarda a ranar Talata a matsayin amsa ga ƙarar da lauyoyin Natasha, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya suka shigar.
Hakan na zuwa ne a lokacin da kwamitin ya shirya dakatar da Sanatar na wani lokaci, wanda hakan ya sa za a dakatar da kowane aiki akan batun har zuwa sadda shari’a za ta bada damar cigaba.
A baya ne dai kwamitin ladabtarwa na majalisar ya gayyaci Sanata Natasha bisa lamarin da ya shiga tsakanin ta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ranar 20 ga watan Fabrairu.
Natasha dai ta samar da rashin tsari ne a majalisar a lokacin da ƙi amince wa yin magana daga kujerarta na zauren, wanda hakan ya sa Akpabio ya dakatar da ita daga gabatar da jawabi, amma kuma ta tirje a karo na biyu.
Daga nan ne majalisar ta uamarci Natasha da ta je gaban kwamitin ƙwarewar aiki da kula da ƙararraki don yin bincike ladabtarwa akanta.
