Majalisa ta yi watsi da koken Sanata Natasha

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kwamitin Ladabtarwa, da Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Dattawa ya yi watsi da ƙarar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi da amfani da ofis ba daidai ba. Majalisar ta bayyana ƙarar a matsayin maras inganci tun daga farko.

Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya bayyana cewa Natasha ta karya ƙa’idar da ke cikin dokar Majalisa ta 40, wacce ta haramta wa Sanata shigar da ƙara da kanta. Bugu da ƙari, an bayyana cewa batun yana gaban kotu, wanda hakan ke sa Majalisa ta rasa ikon sauraron lamarin.

Sanata Akpoti-Uduaghan ba ta halarci zaman binciken ba, yayin da Akpabio ya musanta duk wasu zarge-zarge da ake masa. Ya bayyana cewa bai taɓa cin zarafin kowace mace ba, yana mai cewa an ba shi lambar yabo a matsayin gwamna mafi kyawun fahimta da kulawa da mata a Najeriya.

By ukarofi