Gwamnatin Jigawa za ta ɗauki matasa 9000 aikin tsaro

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse

Gwamnatin Jigawa tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda ta Nijeriya sun ƙaddmar da cibiyar tattara bayanai kan shirin kare makarantun jihar daga barazanar ‘yan ta’adda wato (Safe School Initiative) da nufin bai wa makarantun da ɗalibai da malamai kariya dake aiki a makarantun jihar ta Jigawa.

A jawabinsa lokacin taron, gwamna Umar Namadi na Jihar ta Jigawa ya bayyana shirin gwnanatin Jigawa na ɗaukar matasa 9,000 aikin kare makarantu, asibitoci da kotuna.

A yayin taron na masu ruwa da tsaki an sami gamayyar jami’an tsaro sun yabawa gwamnatin Jigawa bisa irin goyon bayan da ta ke basu ta fuskar aikin tsaro da suke gudanarwa a jihar.

A ƙoƙarin sa na tabbatar da tsaro a makarantu da kuma ɗaukacin Jihar Jigawa, gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi FCA, ya halarci taron masu ruwa da tsaki kan shirin kare makarantu na ƙasa.

Wannan taro na kwanaki biyu, wanda ofishin shugaban hukumar ‘yan sanda na ƙasa ya shirya, ya gudana ne a babban ɗakin taro na Sir Ahmadu Bello da ke sakatariyar jihar ta Jigawa Dutse.

Taron ya tattaro haɗakar jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda, sojoji, jami’an farin kaya, masu sarautar gargajiya, malaman addini, yan ƙungiyoyin tsaro na sa kai, da sauran masu ruwa da tsaki. Kuma an tattauna a kan mahimman batutuwa da suka shafi tsaro domin a sami haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a faɗin jihar domin kare makarantu daga barazanar rashin tsaro da wasu jihohi suka fuskanta , tare da jaddada cewa tsaro haƙƙi ne na kowa da kowa.

Gwamna Namadi, wanda shi ne babban baƙo na musamman a wajen taron, ya bayyana irin ci gaban da jihar Jigawa ta samu a fannin tsaro, wanda ke tabbatar da jihar a matsayin jiha mafi zaman lafiya a faɗin Najeriya.

Ya jaddada cewa irin waɗannan taruka suna da matuƙar muhimmanci domin tsaro da jin daɗin al’umma su ne ginshikan rayuwa.

Ya kuma bayyana wasu daga cikin matakan da gwamnatin Jigawa ke ɗauka don ƙarfafa tsaro a makarantu, kamar kafa cibiyar tattara bayanai da sanya ido kan makarantu, wadda aka ƙaddamar a ranar taron.

A yayin taron, an samar da kayayyakin aiki kamar motoci, babura, na’urorin aikin tsaro, da sauran kayan tattara bayanai daga makarantu. Haka kuma, an ƙulla haɗin gwiwa da kamfanonin tsaro domin ɗaukar matasa 9,000 don tsare makarantu, asibitoci, da kotuna.

Gwamnatin kuma tayi ƙoƙarin kewaye makarantun kwana domin samar da kyakkyawan yanayi na koyo.

A ƙarshe, Gwamna Namadi ya gode wa hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da majalisar sarakunan jiha, malamai, da ƙungiyoyin al’ummar gari bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ya Ƙara da cewa taron zai samar da muhimman shawarwari da za su taimaka wajen Ƙara inganta tsaro a makarantu da sauran wuraren da aka shirya taron dominsu.

By ukarofi