Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu gungun ’yan bindiga sun sace aƙalla ɗalibai mata huɗu da ke zaune a unguwar Paris ƙuarters da ke bayan Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma a Jihar Katsina.
Wani mazaunin garin ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 2:20 na dare, inda ‘yan ta’addan a yawansu ɗauke da manyan muggan makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK-47 suka mamaye yankin cikin kamawa tare da fatattakar ɗalibai mata huɗu.
Ko da yake kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiƙ da jami’an gwamnati har yanzu ba su kai ga amsa tambayar da manema labarai ba, amma an tattaro cewa nan take jami’an tsaro suka garzaya wurin da lamarin ya faru, bayan da aka yi musu waya, amma tuni ‘yan bindigar suka gudu.
Ana dai sa ran za a yi ƙoƙarin zaƙulo waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban da kuma kuɓutar da waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Dutsinma, na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke kan gaba wajen samun matsalar tsaro da fama da matsalar ‘yan fashi da satar shanu duk da matakan tsaro na gwamnati wajen dawo da zaman lafiya a yankin.
