Arsenal ta kafa sabon tarihi a gasar Zakarun Turai

Spread the love

Kwallaye bakwai da ƙungiyar Arsenal ta jefa a ragar PSɓ Eindhoɓen a karawar da suka yi, ya ba ta damar kafa sabon tarihi a gasar zakarun Turai.

Wannan nasara da Arsenal ta samu a filin wasa na Philips, irin ta ce ta farko da wata ƙungiya da ta je baƙunci ta taɓa samu a zagayen ’yan 16 a gasar zakarun Turai.

Bayan tashi daga wasan, mai horas da ƙungiyar ta Arsenal Mikel Arteta, ya ce ’yan wasansa sun yi mura da wannan nasarar da suka samu kan PSɓ ta 7-1.

“Gaskiya abin farin ciki ne, ina farin ciki da kasancewa cikin waɗanda suka kafa wannan tarihi, amma a matsayinmu na ƙungiya mu na buƙatar yin abinda ya fi wannan.”

Rabon da Arsenal ta ci ƙwallaye da yawa haka a wasa, tun karawar da suka yi da Newcastle a gasar Firimiya shekaru 13 da suka gabata, inda ta lallasata da ci 7-3.

A yanzu dai Arsenal ta sanya ƙafarta ɗaya a zagayen dab da na kusa da na ƙarshe a gasar zakarun Turai, inda za ta iya haɗuwa da ɗaya daga cikin Real Madrid ko Atletico Madrid.

By ukarofi