Gwamnatin Tarayya ta amince da kammala tituna huɗu da ta gada daga gwamnatin Buhari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar gudanarwar gwamnatin tarayya a yayin zamanta karo na uku a wannan shekara a ranar Litinin, ta amince da kammala aikin ayyukan titin da ta gada daga gwamnatin da ta gabata bayan zuzzurfan nazari.

Minista ayyuka, Daɓid Umahi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati bayan kammala zaman majalisar.

Ya ce, ayyukan da majalisar ta amince a yi sun haɗa da: aikin mai da titin Odupani-Itu-Idedem zuwa da ke Ikot Ekpene zuwa mai biiyu a faɗin jihar Kuros Ribas da da Akwa Ibom kan Naira biliyan 55 wanda aka bai wa kamfanin kwagila na Decon Construction Nigeria Limited.

“Sai kuma aikin faɗaɗa titin Ibadan-Ilorin zuwa mai biyu wanda ke Ogbomosho a jihar Oyo kan kuɗi Naira biliyan 147 wanda aka bai wa kamfanin kwangila na GRɓe.”

“Sannan akwai ƙarashen titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano wanda ya kai kilomita 164 kan kuɗi Naira biliyan 507.”

“Aikin titi na ƙarshe shi ne na gadar sama a mahaɗar titi ta Abakpa a Enugu wanda za a gina domin rage cunkoson ababen hawa wanda aka bai wa kamfanin kwangila na CCECC kan kuɗi Naira biliyan 24,” inji ministan.

Sannan ministan ya ce kamfanin kwangila na infoWest Nigeria Ltd., ne ya yi nasarar samun damar kammala rukunin aikin titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano.

By ukarofi