Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon kayan tallafin Ɗangote na biliyan N16

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sama da ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya ne za su samu tallafin shinkafa mai nauyin kilogiram 10 daga Gidauniyar Aliko Ɗangote (ADF) bayan ƙaddamar da aikin rabon kayan tallafin da kuɗinsa ya kai naira miliyan 16,000 a wannan shekara ta 2025.

Da yake jawabi a wajen bikin a Kano Arewa maso yammacin Nijeriya shugaban Gidauniyar ta Aliko Ɗangote Foundation Aliko Ɗangote yace rabon tallafin buhun shinkafar mai nauyin kilogram 10 miliyan daya, za a raba su ga mabuƙata a ɗaukacin ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin Nijeriya, aikin da ke zama cikin ƙudirin kamfanin na Ɗangote da gidauniyar ta sa.

Ɗangote da ya samu wakilcin ɗiyarsa Mariya Aliko Ɗangote yace “Wannan aikin rabon tallafi na shekara-shekara aiki ne da ya rataya a wuyanmu da za mu ci gaba da ba da haɗin kai wajen tallafa wa al’umma a wannan yanayi da suka shiga na buƙatar taimako duba da matsalar tattalin arziki, wannan ya nuna yadda muka mayar da hankali wajen tallafa wa al’ummarmu wanda kuma na cikin manufarmu.”

Ɗangote yace sun fara wannan rabon tallafi da Jihar Kano da ke zama mahaifa a gare shi inda daga nan za a kai duk sauran jihohi da ke faɗin Nijeriya.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Kano ke yi wajen tabbatar da ganin tallafi ya kai ga al’ummar da aka yi tanadi domin su wato marasa galihu.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo yace za a raba wannan shinkafa mai nauyin kilogram 10 guda 120,000 ga ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar ta Kano.

Yace wannan kokari ne na Gidauniyar ta Ɗangote a fafutukar ganin ta yaƙi yunwa a tsakanin al’umma.

Yace gwamnati tuni ta kafa wani kwamiti da zai yi aikin rabon kayan tallafin wanda ya haɗar da jami’an ma’aikatu na gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da wasu cibiyoyi da hukumomi a matakin ƙananan hukumomi da hukumar Hisbah da wasu jami’ai na tsaro.

Babbar manajar darakta kuma babbar jagora a Gidauniyar ta Aliko Dangote Zouera Youssoufou, tace wannan rabon tallafin abinci na shekara-shekara wani ɓangare ne na aikin tallafar ayyukan da gwamnati ke yi a ƙoƙarin na yaƙi da talauci da yunwa a tsakanin al’umma.

Wasu da suka amfana daga al’umma marasa galihu a jihar ta Kano sun bayyana farin cikin su da wannan tallafi.

Ilya Yunusa yace “Allah ya ƙaro mana irinsu Aliko Ɗangote kasancewar idan za mu samu irin haka za a rage wahala a cikin al’umma.”

“Allah Ya ƙara masa arziki, gaskiya samun tallafi haka abin farin ciki ne Allah Ya sa sauran masu kuɗi su yi koyi.” A cewar Khalid Muhammad.

Wannan aiki na rabon kayan tallafin shinkafa zai laƙume naira miliyan 16000 kamar yadda jiga-jigan gidauniyar ta Ɗangote suka nunar wanda kuma zai karaɗe duk jihohi na Nijeriya.

By ukarofi