Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Mohamed Matawalle ya bayar da gudunmawar Naira miliyan ɗari biyar ga ‘ya’yan jam’iyyar APC da marasa galihu, a wani ɓangare na tallafin da yake yi na watan Ramadan a jihar Zamfara.
Hakan ya fito ne daga ofishin mai ba da shawara na musamman ga ministan akan harkokin siyasa, Alh. Ibrahim ɗanmaliki yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau jiya Alhamis.
A cewarsa, an zaɓo mutane 200 da suka ci gajiyar tallafin a kowace ƙananan hukumomi 14 da aka ba su Naira dubu ɗari kowannensu.
Ya kuma ƙara da cewa, an kuma raba zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 86 ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, inda ya ce an zaɓo masu ruwa da tsaki 24 daga kowace karamar hukuma ta Zamfara ta yamma inda minista Matawalle ya fito wanda kowane mutum guda ya ci gajiyar Naira 250,000.
Hon. ɗanmaliki ya kara da cewa an kuma zabo masu ruwa da tsaki guda goma a kowace karama hukuma a yankin Zamfara ta Arewa da Zamfara ta tsakiya waɗanda suka ci gajiyar kuɗi Naira 250,000 kowannensu a matsayin tallafin Matawalle domin su gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauƙi.
“Ina son in bayyana cewa, mutane 280 ne suka ci gajiyar kudi Naira 100,000 kowanne wanda Mai girma minista Matawalle ya kashe kuɗi Naira miliyan 280 sannan kuma an raba Naira miliyan 86 ga masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC a karkashin shirin tallafin Azumin Ramadan na Matawalle a jihar,” ɗanmaliki ya ce.
Ya ce matakin na da nufin rage wahalhalun zamantakewar al’umma a cikin wannan wata na Ramadan.
Alhaji Ibrahim ɗanmaliki ya ƙara da cewa, karamcin zai kai ga jami’an jam’iyyar APC, dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa tun daga masu bayar da shawara ta musamman, da manyan daraktoci da suka yi aiki a gwamnatin Matawalle a lokacin yana kujerar gwamnan Zamfara.
