
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ce aikin babban titin Legas zuwa Kalabar da zai lanƙwame Naira tiriliyan 15.6 abu ne da zai bada damar bunƙasa tattalin arziƙi a ɓangarori daban-daban ga ƴan Nijeriya.
Bayanin ya biyo bayan tsokacin toshon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, wanda ya bayyana aikin a matsayin albazzaranci ga dukiyar ƙasa.
Saidai, a yayin kare batun a wata hira da tashar TVC, Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu akan Harkokin Sadarwa, Sunday Dare, ya ce aikin zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da wani shugaba ya taɓa yi a Nijeriya.
A sashi na shida na sabon littafinsa da ya fitar a yayin cikarsa shekaru 88 a duniya, Obasanjo ya bayyana aikin a matsayin ɓarnatar da dukiyar ƙasa da kuma shiga cikin rashawa.
Ya kuma soki Gwamnatin Shugaba Tinubu kan kashe Naira biliyan 21 a gina sabon gidan Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Obasanjo ya ce, ana gudanar da ayyukan da ba su al’umma ke buƙata ba a daidai lokacin da suke cikin halin matsin rayuwa.
A yayin mayar da martani kan kalaman tsohon shugaban, Dare ya ce a lokacin da Tinubu ya ke gwamnan Legas ya buɗe babban titin Lekki-Epe, inda a lokacin ake ganin kamar bai san mai ya ke yi ba. Hakan ya sa aka samu manyan harkokin da ke samar da kuɗaɗe mafiya tsoka.
Ya kuma bada misali da Matatar Ɗangote da tsarin gudanar da harkar kasuwanci a sake, waɗanda sun taimaka wajen samar da ci-gaba ta hanyar haɓaka tattalin arziƙin ƙasa da sauran abubuwa, ya na mai cewa aikin zai zama ɗaya daga cikin muhimman ayyuka a Nijeriya.
