Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Idan akwai wani abu mai tasiri da ɗaure kai da cigaban fasahar sadarwa ya kawo wa duniyar watsa labarai, bai wuce yaɗa labaran ƙarya da jirkita bayanan gaskiya da na bogi ba. Tasirin da wannan matsala ta haifar ya zama fitina mafi girma da ke rikita kawunan hatta ƙwararrun ’yan jarida da masu sarrafa bayanai.
Labaran ƙarya da ake iya samunsu a rubuce, ta hoto, ko ta bidiyo, har ma da sauti, yayin da ake samun ƙwararrun masu tsara labarin ƙarya, su juya labari, yadda zai zama ya dace da abin da suke so, ko domin ɓatar da gaskiya, da raba hankalin mutane. Sukan ƙirƙiro da sauti tamkar na gaske, ko a jirkita hoto ta hanyoyin siddabaru har mutane su yi zaton ko na gaskiya ne, da sauya bidiyo yadda motsinsa da sautinsa za su nuna sak abin da mutane ke rayawa a ransu da gaske ne.
Wannan matsala ta daɗe tana dagula hankalin manazarta da masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa da watsa labarai, a ƙoƙarin su na tantance aya da tsakuwa, da samar da ingantattun bayanai ga jama’a. Saboda sabbin dabaru da siddabaru da masu amfani da fasahar sadarwa ke cigaba da ɓullo da su, masana harkar sadarwa da tace labaru a sassan duniya daban-daban, su ma ba su naɗe hannu sun zuba ido ana gwara kan mutane a tsakanin ƙarya da gaskiya ba. Sakamakon yadda masu fitar da labaran ƙarya kullum suke cigaba da yaɗa ƙarairayi da jirkita gaskiya, suna lulluɓe kura da fatar akuya, ya sa aka shiga fito da hanyoyi na ilimi da dabaru irin na masu abu da abin su, domin kawar da ƙarairayi da fahimtar da jama’a.
Kodayake, waɗannan hanyoyi na ilimi da dabarun zamani da ake amfani da su don yaƙi da yaɗa ƙarya da jirkita gaskiya da turanci ake yaɗa su, ya sa wani matashin ɗan jarida mai bincike kan labaru da al’amuran yau da kullum, mai suna Alhassan Bala, ɗan asalin Jihar Kano kuma mazaunin Abuja, kafa cibiyar tantance gaskiyar labaru da wayar da kan jama’a game da fasahar sadarwa, wanda ya sanyawa suna Alƙalanci, mai aiki da harshen Hausa.
A tsakanin watanni 6 zuwa 7 da fara gabatar da ƙananan bidiyoyi da yake fitarwa yana fayyace gaskiyar labaran da aka jirkita ko aka shirga ƙarya a kansu, a zaurukan sada zumunta na Facebook, Tiktok, WhatsApp, Instagram, ɗ da sauransu. Jama’a da dama sun ilimantu da abubuwan da yake yaɗawa, kuma an fara ganin sauye-sauye, sakamakon yadda masu yaɗa irin waɗannan labaran ƙarya suke yin mi’ara komabaya, wajen sauke irin labaran da suke yaɗawa, don jan hankalin jama’a ga shafukansu, waɗanda ba na gaskiya ba ne. Alhamdulillahi!
A kan wannan ƙoƙari, Alhassan Bala, har ƙasar Belgium da ke nahiyar Turai ya je samun horo da ƙarin ilimi, akan dabarun gano yadda ake amfani da ra’ayoyin siyasa, al’ada ko addini, don a juya wani labari ta yadda zai ja hankali, ko ya tunzura jama’a, don wasu ’yan tsiraru su cimma burin su. Wannan horo da ya samu babu shakka ya ƙara masa gogewa kan yadda harkokin sadarwa ke tafiya a duniya, ba a Afirka ko Nijeriya kaɗai ba. Kuma muna ganin hakan a zahiri cikin sabbin ayyukan da yake fitarwa na baya bayan nan.
Babu shakka Alƙalanci na yin alƙalanci da kyau, kuma jama’a na cigaba da nuna yabawa da jin daɗin yadda yake feɗe biri har bindi domin fayyace gaskiya, da zarar wani sabon labarin da ba shi da tushen gaskiya ko wani bidiyo da aka shirya don ɓoye gaskiya ko neman hautsina hazo ya bayyana a zaurukan sada zumunta, musamman ma kuma in da Hausa aka yi shi. Wani abin burgewa kuma shi ne wannan ɗan jarida bai tsaya kan tantance gaskiyar labari kawai ba, lokaci zuwa lokaci yana gabatar da gajerun bitoci kan yadda masu bibiyar shafinsa za su ƙaru da ilimi game da yadda harkar sadarwa take, da yadda za su riƙa gane gaskiyar labari da kansu.
Ba a Nijeriya kaɗai ba, hatta a Nijar da sauran ƙasashen Afirka inda ake da Hausawa ko masu mu’amala da harshen Hausa, ana samun masu bibiyar shafukan Alƙalanci, domin gano gaskiyar wani labari da ya ɗaure musu kai ko suke da kokwanto a kansa. Wasu ma kai tsaye suke tuntuɓar sa don sanin ingancin wani labari da suka karanta, ko hoton da suka gani, ko wani bidiyo da ake yaɗawa. Ta tabbata dai yanzu mutane sun fara wayewa, an daina ɗaukar labari daga yadda aka karanta ko aka ji shi, sai an bincika domin gano sahihancinsa, da inda ya fito, kafin ma su jira alƙalin Alƙalanci ya gaya musu.
A cewar Alhassan Bala, ‘A yayin da jama’a suka fahimci yadda za su tuhumi ingancin labari, inda ya fito, da zargin rashin gaskiya a cikin rahoto, hoto ko bidiyon da aka tsara, babu shakka an samu cigaba sosai. Sun samu zarafin da za su kare kansu daga fargaba, tsoro, ko wata rashin yarda da za ta iya tasiri a tunaninsu da zuciyoyinsu.’
ɗaya daga cikin ƙalubalen da al’ummarmu ke fama da ita, ita ce ta rashin wadatattun ƙwararrun da za su ilimantar da su yadda za su ƙauracewa jita-jita da sauraron gulmace-gulmace da ake yaɗawa da nufin ɓata sunan wani ko aibata shi a wajen jama’a, ba tare da ƙwaƙƙwaran bincike ba. Wannan dalili ne yake bai wa labaran ƙarya sauƙin samun karɓuwa a wajen mutanen mu, duk inda ra’ayin jama’a ya karkata ko gaskiya ne ko ba haka ba ne, nan kowa yake bi. Wannan ne tunanin da Alhassan Bala yake son canzawa, kuma Alhamdulillahi ana samun nasara.
Akwai buƙatar jama’a su rungumi wannan sabuwar fasaha ta tantance gaskiyar labari da yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, da bai wa mutane irin su Alhassan Bala goyon baya don faɗaɗa wannan ilimi da tona asirin masu yaɗa ƙarairayi da jirkita gaskiya. Sannan ina ƙara kira ga hukumomi da sauran masu faɗa a ji su tallafawa irin wannan ƙoƙari da Alƙalanci ke yi, wajen taimaka masa da sauran abokan aikinsa ’yan jarida, da muhimman bayanan da suke buƙata, domin tantance gaskiya, da fitar da rahotanni masu inganci.
