Ɓullar wata cuta ta yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’a biyar a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata cuta da ba a kai ga sanin haƙiƙanin ta ba a Jihar Kebbi, ta yi sanadiyyar mutuwar wasu ɗalibai guda biyar da ke karatu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar dake Aliero (KSUSTA).

Wasu ɗaliban da suka buƙaci a ɓoye sunayensu, sun shaida wa manema labarai cewa huɗu daga cikin ɗaliban da suka kamu da cutar sun rasu ne a makon da ya gabata, yayin da ɗayan kuma ya rasu a ranar Lahadi bayan wani zazzaɓi na lokaci guda.

Wani shaida ya ce, a makon da ya gabata ne jami’an Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka ziyarci makarantar, inda suka wayar da kan al’umma game da haɗarin cutar sanƙarau.

Saidai, ba su tabbatar da cutar a matsayin abinda ya sabbaba mutuwar wasu ɗalibai biyu a makarantar gabannin zuwansu ba.

Rajistiran jami’ar, Maimaru Alhaji Tilli ya shaida wa manema labarai cewa sun tabbatar da mutuwar ɗalibai huɗu, lamarin da ya sa ya aika wa Kwamishinan Ilimin Manyan makarantu, Isa Abubakar Tunga saƙon neman hanyar da za a magance iftila’in.

Tuni dai ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar ɗaliban jami’ar ya ce sun rubuta wa hukumar gudanarwa saƙon neman a rufe jami’ar don ƙauce wa cigaba da faruwar al’amarin nan gaba.

By Babaji