Koyarwar  malaman ƙasar Hausa a da da yanzu

Spread the love

Daga MUBARAK UMAR

A shekarun baya, malamai sun fi mayar da hankali kan koyar da al’umma ibada, wadda ita ce tushen addini da za ta tsallakar da mutane ranar lahira.

Makarantu Islamiyya da majalisin karatu, za ka samu duk an fi mayar da hankali kan ibada, amma a yanzu, an fi mayar da hankali kan wasu abubuwa da ba su kai ibada muhimmanci ba, matasa da yawa ba su san, ko sun manta yadda ake gyaran sallah idan aka samu akasi ba.

A yankin nan namu aka samu yaron da a kotu aka tambaye shi shika-shikan Musulunci, kowa ya ga amsar da ya bayar, wadda mutane suka yi ta dariya, maimakon kuka.

A cikin azumin nan, na bi wani sallah a masallaci (Sallar Magriba), a ɓoye ya yi karatun raka’ar farko da ta biyu, sai da muka idar na yi masa bayani.

A masallacin Juma’a, wani ya yi sallah kusa da ni, raka’a ɗaya ya samu, da aka yi sallama bawan Allah ya tashi ya ciko raka’a uku, maimakon ɗaya.

Rafkanuwa za ka ga mutum ya yi, amma bai san ƙabli ko ba’adi zai yi ba.

Malamai a cikin al’umma tamkar masu mulki ne, Allah ne ya ba su ilmi, haƙƙinsu ne su koyar da al’ummar abinda zai amfane su duniya da lahira.

Mun tsinci kanmu a zamanin da karatu ya yawaita, littattafai bila’adin, a faɗi mujalladi da lambar shafi, amma duk da haka ilmi ya yi ƙaranci a cikin al’umma, saboda an wawantar da hankulan mutane. Barkanmu da shan ruwa!

Malam Mubarak, wanda ake kira da Mubarak Khan, ya wallafa ne a shafinsa na Facebook cikin makon nan

By ukarofi