Aure da saki a fim: Gangan ko gaske?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Maganar aure ko saki a fina-finan Kannywood ta fara zama abin tattaunawa tsakanin malamai a yan shekarun nan. A bara, wasu malamai sun yi bayanin fatawar cewa Idan ka saki mace a fim ta saku. A bana ma, wannan zance ya sake dawowa ana ta cece-kuce a kansa, har ma da zancen ridda a fim.

Na farko dai abinda ya kamata mu fara ganewa shine kamar yadda Manzo ya fada “Haram a bayyane ta ke, haka shi ma halal a bayyane ya ke”. Sannan Allah ya bada hukunce-hukunce cikin ƙurani wadanda da su malamai ke gwamutsawa da wasu hadisai gwargwadon fahimtarsu sannan su bada hukunci. Ta wannan tsari, sannu a hankali magabata su ka gina shari’ar musulunci, akasari karkashin mazhabobi.

Yawancin malamai sun tafi kan cewa hukunce-hukuncen addini sun cika babu wani sabon hukunci da za a iya bijiro da shi, ko kuma dole sai dai kawai a bi hanyar magabata, amma na yanzu babu sauran ijtihadi da zakulo hukunci. Kowacce kasar musulmi, banda ta mu, za ka samu su na da majalisar fatwa domin tunkarar duk wata sabuwar matsala da ka iya bijirowa.

Zamani na cacccanzawa yayin da ya ke bijiro da sabbin matsaloli wadanda dole a samar musu hurumi na shari’a. Wannan tsari na gina ijtihadi a doron ƙurani da Sunna da shi aka gina shari’ar musulunci kuma da shi ya kamata a ci gaba, amma wasu malamai sun kafe duk abinda magabata ba su ambato ba, to kawai a yi watsi da shi.

Gajeren misali na bukatuwar malamai dole su rika ijtihadi domin samar da sabbin fatawa ko yin karo da abinda aka sani daga magabata na iya tasawo a koda yaushe. Misali Idan ka dauki hukunci zubar da ciki, wanda karara ya sabawa ƙurani da Sunna, amma misali yadda Yan ta’adda ke yi wa mata fyade har su sami ciki, shin menene hukuncin mace da ta sami kanta a wannan yanayi? Za ta iya zubar da wannan ciki? Abu ne da ke bukatar malamai yin ijtihadi da bada fatawa.

Idan mu ka koma kan sakin aure ko daura shi a cikin Fim wanda wasu malamai ke ganin halastacce ne, ya kamata mu dubi abin ta mahanga da yawa.

Na farko dai shi Fim a tsarinsa kowa ya hakkake cewa gangan ne ba gaske ba, kuma a farko farkon fiƙihun musulunci, abinda ya fara koya mana shine “Dukkan ayyuka sai da niyya” Wanda aka zakulo daga hadisin Umar cikin Al Nawawi da kuma fassarar aya ta 100 a suratun Nisa da ke nuna mahimmancin niyya a game da aiki. Shin fatawar saki a fim, ta yi karo  ko kuwa ta yi daidai da wannan aya da hadisai (Bukhari da Muslim duk sun ruwaito).

Abu na biyu da ya kamata a dora kafin wannan fatawa shine: Duk mazhabobin nan guda hudu sun gitta sharudda wadanda sai sun cika aure ke tabbata. Cikin wadannan sharudda akwai:

1. Sadaki, wanda ƙurani ya tabbatar a matsayin sharadi cikin ƙ4:4

2. Shaidu: Wanda aka zakulo daga ayoyin Baƙara ƙ2:282 da Al Talaƙ ƙ65:2

3. Amincewar ma’aurata: Wanda ayar Nisa’i ta kawo ƙ4:19

4. Wali: Aure na ginuwa ne ta hannun wali

Shin aure a Fim ya cika duk wadannan sharudda?

Allah ya gargade mu cikin suratul Maida

ƙ5:8 “Ya ku wadanda su ka yi imani….kada kiyayya da wasu mutane su dauke ku, a kan ba za ku yi adalci ba”

Wato idan ka lura, wasu malamai a kasar Hausa na far ma Yan Fim, a duk wata kafa da su ka samu. Da a ce haka su ke wa Yan siyasa da watakila mun ga canji. Akasarin malamai na yiwa masana’antar Kannywood kudin goro, maimakon ajiye komai a muhallinsa kamar yadda waccan aya ke umarta. Don baka kaunar wani, idan gaskiya ta zo ko a kansa, wajibi ka bi ta. Kuma kowacce sana’a ko jinsin al’umma akwai baragurbi, amma rashin adalci ne ka yi kudin goro. Allah ya gina tsarin Dan Adam a bigire biyu

ƙ90:10 “Kuma ba mu shiryar da shi (Mutum) ga hanyoyi biyu ba?

Mu na da saurin mantuwa, amma a garin Kano, irin badala da aka sami wasu malamai a kai, da Yan Fim ne da sai an tsire su. Domin akwai babban malamin jummu’a da aka kama da luwadi a cikin harabar masallacinsa har gaban Sarkin Kano marigayi Ado maganar ta je. Sannan akwai wani malamin da ya far ma Yan Fim amma aka kama shi a titi ya na kokarin yin lalata a cikin mota da yarinya wadda ya ke rikewa a gidansa a matsayin yarsa. Wannan zai sa a yi tur da malamai? Ko kadan, abin sani kawai ko a ina akwai nagari da mugu.

Adalcin musulunci shine kada don baka son wani ka gaza yi masa adalci kamar kowa. Auren fim, auren wasa ne kuma har abada a wasa zai zauna domin fadakarwa kawai. Aure ne da bai cika kowane irin sharadi da malamai da kansu ke koyarwa a babin aure karkashin tsarin duk mazhabobin nan guda hudu ba.

Malamai a Turkiya, Egypt da Saudia a yanzu, sun gane mahimmancin Fim a rayuwar Dan Adam, don haka suka soka kansu a ciki harkar domin tsaftace ta a wadannan kasashen na musulmi. Ba na mantawa a lokacin dambarwar Fim ɓillage a Kano, a wani taro da muka yi a Shari’a commission, tare da su Malam Khalid, Iyantama da wasu Yan Fim da wasu malamai, na yiwa Malam Abduljabbar (lokacin ya na commissioner na commission din) irin wannan tambayar cewa babu film ɓillage a kasashen larabawa? Shin shigar malamansu cikin harkar fim, bai basu damar tsaftace ta a wadancan kasashen ba?

Wannan masana’anta ta Kannywood, babu wata masana’anta da ke samawa matasa ayyukan yi irinta a Arewa a yanzu. Kuma bincike ya nuna cewa akwai kimanin sana’oi 26 da ke alakantuwa da masana’antar. Wajibi ne malamai, gwamnati da attajira su karkata hankulansu wajen saka hannu sosai a wannan masana’anta domin ci gaba da samar da ayyukan yi, kudaden shiga da tsaftace ta. Yan siyasa da su ka fi kowa hankali a Najeriya, wajen bin hanyoyin biyan bukatunsu, ba ku ga yadda su ka rungumi wani sashe na masana’antar Fim ba, kuma suke cin moriyarsa? To haka kowa zai iya cin moriyar wannan masana’anta idan an inganta da tsara tsaftace ta, ba mayar da ita abin tsangwama ko saniyar ware ba.

Jummu’a Mubarak… A sha ruwa lafiya.

Malam Ali Abubakar manazarci ne kuma mazaunin Jihar Kano

By ukarofi