
Daga BELLO A. BABAJI
A yammacin ranar Laraba ne wasu ƴan bindiga suka kashe Muhammad Adamu, wanda shi ne shugaban Miyetti-Allah – ƙungiyar Fulani Makiyaya (MACBAN), a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi dake Jihar Filato.
Shugaban MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo ya bayyana hakan ga manema labarai a Jos, inda ya ce ƴan bindigar sun kai hari ne wa mamacin a gidansa, jim-kaɗan bayan shan ruwa.
Ya ce, sun harbe shi ne sau adadi mai yawa, wanda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa a wajen da abin ya faru.
Ya kuma yi alla-wadai da aukuwar lamarin tare da kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki wajen gudanar da bincike mai zurfi.
Ya ƙara da cewa, lallai akwai buƙatar a kamo waɗanda suke da hannu aciki da tabbatar da cewa sun fuskanci hukuncin doka.
I’zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba samu ji ta bakin Kakakin ƴan sandan jihar, Alfred Alabo ba domin bada ba’asi akan al’amarin.
