Benue: ‘Yan sanda sun kashe ƴan bindiga da ƙwato makamai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Rundunar ƴan sanda a Jihar Benue, sun yi nasarar kashe wasu ƴan bindiga da ƙwato makamai a yayin atisaye daban-daban.

Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya yi alhinin rasuwar ɗaya daga cikin jami’an, wanda rasa ransa a yayin daƙile ayyukan ƴan bindigar.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an gudanar da atisayen ne a ƙarƙashin umarnin Sufeton ƴan sandan.

Ya ce, an yi hakan ne a ƙoƙarin jami’an na ganin an daƙile ayyukan garkuwa da mutane da fashi da wasu manyan laifuka a Nijeriya.

Jami’an rundunar a jihar sun ɗauki matakan atisaye ne la’akari da ayyukan ta’addanci da ke faruwa a wasu sassanta, inda a ranar 19 ga watan Maris suka yi arangama da wasu ƴan fashi a Ƙaramar Hukumar Buruku a lokacin da ƴan fashin suka nufi wata mafaka a yankin Agwabi, lamarin da ya yi sanadin hallaka 12 daga cikin su.

Haka kuma jami’an sun yi nasarar ƙwato bindigu ƙirar ‘pistol’ ta gida guda bakwai da AK47 guda uku da kama ɓarayi biyar da wasu 32 da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne.

Adejobi ya kuma ce, Sufeto Egbetokun ya jinjina wa jami’an nasu bisa jarumta da sadaukarwa da suka nuna wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ke fama da ayyukan ta’addanci.

Ya ƙara da cewa, rundunar za ta cigaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa, ya na mai kira ga al’umma da su ruwaito duk wani abin zargi ga jami’an.

By Babaji