Kotu ta hana INEC amsar ƙudirin yi wa Sanata Natash kiranye

Spread the love

Kotun Tarayya da ke Lokoja ta bayar da umarnin hana hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) karɓar ƙorafe-ƙorafen da aka shigar don fara tsarin kiranye ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Rahoton da Blueprint Manhaja ta samu ya nuna cewa ƙoƙarin yin kiranye ga sanatar ya ƙara tsananta a ranar Alhamis, inda ƙungiyoyi daga Kogi ta tsakiya suka ci gaba da nuna goyon baya ga tsarin.

Amma wata ƙungiyar ‘yan asalin Ebira ta musanta cewa tsarin kiranyen na da alaƙa da kuɗin da wasu abokan hamayyar siyasa na Akpoti-Uduaghan suka bayar.

Kotun ta bayar da umarnin ne a ranar Alhamis ta hanyar ƙarar gaggawa da aka shigar gabanta.

Kotun ta kuma haramta wa ma’aikatan INEC, wakilai, ko duk wanda aka ɗora wa alhakin aiwatar da wannan aiki karɓar kowane ƙorafi da ke ɗauke da sa hannun bogi na wasu mambobin yankin Sanatan Kogi ta tsakiya har sai an kammala sauraron buƙatar a ranar 6 ga Mayu, 2025.

Lauyan da ya gabatar da ƙarar, Smart Nwachimere, daga ofishin West-Idahosa, SAN & Co., ya ce wannan umarni zai taimaka wajen tona asirin wasu da ke ƙoƙarin amfani da ƙarfi wajen tunbuke sanatar.

By ukarofi