Gwamnatin Bauchi ta yi ƙarin haske kan ɗage bikin hawan sallah

Spread the love

Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi ƙarin haske kan ɗage bikin hawan Sallah na bana, tana mai cewa shawarar ɗagewar ta fito ne daga Majalisar Masarautar Bauchi, ba tare da ssaninsu gwamnati ba. Gwamnati ta bayyana cewa ta riga ta yi cikakken shiri na tsaro da sauran ayyukan da suka dace domin gudanar da bikin cikin nasara, amma daga bisani aka samu sanarwar ɗagewa daga masarauta.

A wata sanarwa da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, ya ce duk da takaicin yadda aka yanke shawarar ba tare da haɗin gwiwa ba, gwamnatin jihar ta girmama matsayar masarauta domin mutunta al’ada da jagorancinta. Gwamnati ta kuma yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace domin kaucewa irin wannan rikici a nan gaba, musamman kan harkokin da suka shafi al’ummar jihar.

Duk da ɗage hawan, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya aikewa al’ummar Bauchi da saƙon barka da Sallah, yana mai fatan a yi bukukuwan cikin kwanciyar hankali da lumana. Ya kuma bayyana muhimmancin bikin hawan Sallah wajen haɗa kan al’umma da nuna alfaharin al’adun gargajiya na Bauchi, tare da jan hankalin masu yawon buɗe ido daga ciki da wajen ƙasa.

By ukarofi