An kori ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ibadan daga, Shooting Stars daga gasar Kofin Nijeriya ta shekarar 2025 bayan da aka same ta da laifin shigar da ‘yan wasan da ba su cancanta ba a wasansu na farko da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zamfara United FC.
Oluyole Warriors, waɗanda tun farko suka tsallake zuwa zagaye na 32 sakamakon rashin halartar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zamfara United FC, yanzu an kore su daga gasar.
Wata wasiƙa daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) mai ɗauke da sa hannun daraktan gasar Ruth David, ta bayyana cewa Shooting Stars ta saka ‘yan wasa biyar da ba su yi rajista ba a wasan nasu.
A cewar wasiƙar “Ya zo mana cewa kulob ɗin ta sanya ‘yan wasa biyar da ba su cancanta ba waɗanda ba su da rajista da NFF a wannan bugu na gasar.”
‘Yan wasan da ba su cancanta ba sun haɗa da: Samuel Okon (Jersey No 21) Sodiƙ Ibrahim (Jersey No 27) Ephraim Nwachukwu (Jersey No 20) Nonso Nzediegwu (Jersey NO 23) da Ukeme Williams (Jersey No 5).
Hukumar ta NFF ta ci gaba da zargin cewa lasisin ‘yan wasan da waɗannan ‘yan wasan ke amfani da su na jabu ne.
