Daga AISHA ASAS
A makon da ya gabata ne Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya ta shiga komar Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Zagon ƙasa, wato EFCC ta shiyar Jihar Kano, inda suka kama jarumar da laifin wulaƙantawa da lalata takardun Naira.
Hukumar ta yi ram da jaruma Murja Ibrahim Kunya ne kan laifin fesa takardun Naira da ta yi don jin daɗi a lokacin da take zaune a ɗakin otal da ke cikin Tahir Guest Place a Kano.
Za a iya kiran kamen da ‘faɗuwa ta zo daidai da zama’, domin ya faru ne a daidai lokacin da hukumar ta EFCC ke farautarta bayan tsallake sharaɗin belin da hukumar ta bayar nata tsawon wata ɗaya da ta wuce.
Idan mai karatu ya kasance ma’abuci shiga kafafen sadarwa, kuma mai yawan bibiyar lamarin da ya shafi jaruman TikTok irin su Murja Kunya, ba zai rasa ji ko ganin rahoton kamen farko da hukumar ta EFCC ta yi wa jarumar ba a watan Janairun wannan shekaran.
Hukumar ta damƙe ta ne kan lefin karya dokar Babban Bankin Najeriya, CBN. Ita wannan dokar ba wata ba ce face dokar da ta haramta cin zarafin takardun Naira.
Hukumar ta bayar da belin ta na wucin gani, ma’ana har zuwa lokacin da za a gurfanar da ita a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano, saidai a lokacin da aka kai ranar gabatar da ita gaban kuliyya, jaruma Kunya ta ari na kare, don haka ta bijirewa tsarin shari’a.
Bayan kwashe tsawon makwanni ana gudanar da bincike kan lamarin, hukumar ta yi nasarar cika hannu da jarumar a karo na biyu, wanda ya yi daidai da ranar Lahadi, 16 ga watan Maris, 2025, wanda a take suka garƙame ta a ofishin hukumar na nan shiyar Kano, inda za ta kasance a tsare zuwa lokacin da za a gurfanar da ita gaban kotu.
