Daga GAMBO ISA
Shugaban ƙaramar Hukumar Gwoza, a Jihar Borno, Honorabul Abba Shehu Timta Adamu ya yaba wa gwamnan jihar, Maigirma Babagana Umar Zulum kan cigaban jihar da yake samarwa a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ciki har da jaridar Blueprint a Abuja.
Ya zayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnan ya samu a ɓangaren cigaban ɗan adam, samar da ababen more rayuwa da raya ƙasa, noma da kiwo, ilimi, cibiyoyin kiwon lafiya, gina manyan tituna a ƙananan hukumomi 27 da sauransu.
Honorabul Shehu Timta, ya cigaba da bayyana wasu nasarorin da suka haɗa da, wayar da kan mutane, shirye-shirye kamar gina kasuwar zamani da suka ƙunshi shaguna 12 a ƙaramar Hukumar Gwoza da sauran ƙananan hukumomin jihar.
Honorabul Tima ya yaba wa aikin gina titunan garin Gwoza da sauran ƙananan hukumomin jihar, inda ya ce kuma a fannin yaƙi da ƙungiyar Boko Haram da masu tada ƙayar baya, gwamnatinsa ta bai wa jami’an tsaro ƙwarin gwuiwa ta hanyar duba yanayin tsaro tare da yin kira ga al’ummarsa da su kasance masu ƙaunar zaman lafiya a kodayaushe.
Honorabul Abba Shehu Timta ya ce Gwamna Babagana Umar Zulum ya yi tasiri ga rayuwar marasa galihu da gajiyayyu a ƙaramar hukumar Gwoza da sauran ƙananan hukumomin jihar, inda ya buƙace su da su tallafa wa da yawa daga cikin shirye-shiryensa.
Honorabul Shehu Timta ya buƙaci al’ummar ƙaramar hukumar Gwoza da su shiga cikin shirye-shiryen shirin noma da kiwo na gwamna, inda gwamnati ta samar da kayan amfanin gona don yin noma da kiwo kyauta.
Ya kuma shawarci matasa da su kasance jakadun yankin nagari a kodayaushe, inda ya buƙace su da su bi dokokin tsarin mulki da dokokin ƙasa, su guji shan miyagun ƙwayoyi, su riƙa saurara da mutunta dattijai a cikin al’ummarsu ko yankinsu, kana su rungumi sana’o’in hannu don dogaro da kawunansu.
