Gwamna Mutfwang ya yi buɗe-bakin Ramadan da Musulmi a Jos

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI Jos

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya yaba wa gudunmawar da al’ummar Musulmi suke bayarwa ga cigaban zaman lafiya da tsaro a jihar tare da jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani mai son tayar da fitina ya samu nasara ba.

Ya ce, daga yanzu babu wani yanki na Jos da za a ce mallakar Musulmi ne ko na Kirista, har kuma ana barazana ga rayuwar wani ko wasu a yankin.

“Jihar Filato ta kowa ce, kuma babu wani yanki da za a ce wani ba shi da ƴancin shiga ko zama. Ba za mu sake bari wasu marasa son zaman lafiya su sake mayar da mu baya ba.”

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin liyafar buɗe-baki da ya shirya wa al’ummar musulmi a fadar gwamnatin jihar albarkacin azumin watan Ramadan da aka gudanar.

Ya nemi Musulmi da Kirista su cigaba da nuna halayen ƙwarai da tallafa wa mabuƙata, kamar yadda suka riƙa nunawa cikin watan Ramadan.

Mai Martaba Sarkin Kanam, Muhammadu Mu’azu ya yaba wa Gwamna Mutfwang, bisa yadda ya shirya wannan liyafar buɗebaki da ƙoƙarin da yake yi na gudanar da ayyukan raya ƙasa a yankunan musulmi ba tare da nuna bambanci ba.

Ya jaddada samun haɗin kan musulmi da goyon bayan su ga gwamnati a kodayaushe.

By Babaji