Gwmanaitn mulkin sojin Burkina Faso ta rusa ƙungiyar yan jaridar ƙasar (AJB), kwana ɗaya bayan ta kama biyu daga cikin shugabannin ƙungiyar waɗanda suka nuna rashin amincewarsu dangane da yadda sojojin ke tauye ƴancin faɗin albarkacin baki a ƙasar.
A sanarwar da Ministan Yaɗa Labarai Emile Zerbo ya fitar, ta ce an rusa ƙungiyar ce saboda ta gaza cika ƙa’idojin ƙafa ƙungiya kamar yadda wata doka da aka kafa a ƙasar a 2025 ta shata, kuma a cewarsa tun a wannan shekara ce ya kamata ƙungiyar ta daina gudanar da ayyukanta.
A ranar Juma’ar da ta gabata, shugaban ƙungiyar AJB Guézouma Sanogo ya fito fili ƙarara inda ya yi tir da Allah wadai dangane da irin matakan da gwamnatin mulkin sojin ƙasar ke ɗauka kan kafafen yaɗa labarai na cikin gida da kuma ƙetare.
Sanogo, wanda ke aiki ƙarkashin hukumar rediyo da talabajin mallakin Burkina Faso (RTB), ya zargi waɗannan kafafe da kuma kamfanin dillancin labarai na ƙasar a matsayin kafafen yaɗa farfagandar gwamnati.
Bayan wannan furuci ne, jami’an tsaro da Hukumar Leƙen Asiri ta ƙasar suka kama Guézouma Sanogo shugaban ƙungiyar da mataimakinsa Boukari Ouaba, da wani ɗan jarida Luc Pagbelguem, da ke aiki da tashar talabijin mai zaman kanta BF1, kuma har yanzu ba wanda ya san inda ake tsare da su.
Tuni dai ƙungiyar kare hakkin ƴan jarida a duniya Reporters Sans Frontiers ta yi kakkausar suka a game da wannan lamari, tare da bayyana matakin a matsayin yunkuri don tozarta aikin jarida da kuma murƙushe duk wani mai ra’ayin da ya sha bambam da na gwamnatin mulkin sojin Keftin Ibrahim Traore.
