Gwmanatin Jamhuriyar Nijar ta ce har yanzu ƙofofinta suna a buɗe domin sulhuntawa da kamfanonin man fetur na ƙasar China, amma sai sun cika wasu sharuɗa ciki har da bai wa Nijar damar taka gagarumar rawa a duk wasu batutuwa da suka shafi haƙa, tacewa da kuma fitar man fitar da mai zuwa ƙetare.
Matsala tsakanin Nijar da kamfanonin China uku da ke gudanar da harkar man fetur a Nijar ta fito fili ne, bayan mahukunta suka umarci shugabannin kamfanoni da su fice daga ƙasar, tare da kwace lasisin otel ɗin da ke matsayin masauki ga illahirin Chinawa da ke aiki da waɗanda suka zuba jari a wannan ɓangare.
Gwamnatin Nijar ta ce dole ne su mutunta dokokin ƙasar, da suka haɗa da samar da daidaito ta fannin albashi, da daidaito ta fannin raba manyan muƙamai a tsakanin ma’aikata ƴan Nijar da kuma takwarorinsu ƴan asalin ƙasashen ƙetare, sai kuma bai wa kamfanonin cikin gida Nijar damar samun kwangila a harkar man fetur.
Wani dalili a game da korar shugabannin kamfanonin ƴan China shi ne, yadda ba sa bai wa injiniyoyi ƴan Nijar damar samun gogewa a fannoni daban daban, wanda hakan zai ba su damar iya sarrafa na’urorin haƙa da tace man fetur a nan gaba. Kuma a cewar gwamnatin Nijar, wannan batu ne da ke ƙunshe a yarjejeniyar da ta haɗa ƙasashen biyu kusan shekaru 14 da fara fitar da wannan makamashi a ƙasar.
Wata babbar matsalar da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke neman zaunawa domin warwarewa tsakaninta da ƴan China ita ce ƙarin haske a game da yadda aka bayar da kwangilar shimfida bututun mai daga ƙasar zuwa Jamhuriyar Benin, tare da neman a bai wa ƴan kasuwar Nijar damar saka jari a wannan kamfani.
