Amurka da Ukraine za su gana a Saudiyya kwana guda bayan tattaunawarsu da Rasha

Spread the love

Amurka da Ukraine za su gudanar da wata gajeruwar tattaunawa a Saudiyya, kwana guda bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Rasha, wacce ta maida hankali kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine, duk da cewa ba su sanar da matsayar da suka cimma ba.

Shugaban Amurka Donald Trump dai na ta ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen rikicin Rasha da Ukraine da aka kwashe sama da shekaru uku ana yi, inda ake fatan zagaye na ƙarshe na tattaunawar ta Riyadh, za ta ba da damar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

A farkon wannan watan ne dai Ukraine ta bayyana amincewarta da buƙatar Amurka na yarjejeniyar tsagaita wutar, sai dai Rasha taƙi amincewa da hakan, lamarin da ya sanya Kyiɓ da sauran kawayenta na Turai suka zargi Moscow da rashin son zaman lafiya.

Bayan ganawar da aka yi tsakanin wakilan Amurka ta na Rasha a ranar Litinin, kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskoɓ, ya ce ba za a sanar da cikakken rahoton tattaunawar ta su ba, har sai an kammala bitarsa.

Rasha dai ta ce za ci gaba da tattaunawar tsakaninta da Amurka, sai dai ba a bayyana ranar da za a ci gaban ba.

Wata kafar yaɗa labaran Rasha ta ce nan gaba ne Rasha da kuma Amurka za su fitar da sanarwar haɗin gwiwa kan matsayar da suka cimma a tattaunawar ta su.

By ukarofi