
Daga BELLO A. BABAJI
Wani al’amari da ke kama da wasan kwaikwayo ya faru a yayin da ake tsaka da shari’ar da ke tsakanin Barista Kabir Turaki (SAN) da Hadiza Baffa, a yayin da Alƙali Iyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya ya koka kan yadda wani lauya ya gabatar da kansa ba bisa ƙa’ida ba.
Lauyan ya hallara ne a madadin wanda ke kare Hadiza Baffa, wanda kuma ba shi ne ya shigar da ƙarar ba, sannan bai taɓa zuwa wajen shari’ar ba.
A ranar 24 ga watan Maris ne wani mai suna Pius Sunday Okeoma ya shigar da ƙorafi akan Majalisar Alƙalai ta Ƙasa (NJC) kan cewa alƙalin da ke hukunci game da ƙararsu ya na ɗaukar ɓangare da nuna son kai, don haka ya nemi NJC da ta sauya shi, lamarin da ba zai yiwu ba sakamakon NJC ba ta da ikon yin hakan.
Alƙalin ya bayyana lauyan a matsayin wanda ka iya fuskantar ladabtarwa daga majalisar kasancewar ya saɓa wa dokar kotu.
A wani labarin kuwa, lauyan da ke kare ɓangaren Turaki, ya ƙalubalanci sahihancin takardar da ɗaya daga cikin ƴan sandan da ke bincike ya gabatar, inda ya ce an samu fasfot guda biyu na mabanbanta mutane, don haka ya nemi kotun da ta yi hukunci.
Haka kuma, an samu soke-soke daga ƙungiyoyi masu zaman kansu ganin yadda ƴan sanda suka gaggauta gudanar da bincike ba tare da jin ra’ayoyi akan wanda ake zargi ba.
Ƙungiyar ‘Arewa Renaissance Group’ ta hannun Usman Abba, wanda shi ne Kodinetanta, ta ce gwajin DNA da aka yi da bai wa Hadiza Baffa da tawagarta ba tare da sanar da Turaki ba, da kuma ɗora shi a kafar sada zumunta, tauye haƙƙin ɗan-adam ne da aka yi wa Turaki.
