Natasha ta gudanar da gangami Kogi duk da dokar hana taro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya, ta sauka a mazaɓarta da ke Jihar Kogi a Arewacin Nijeriya.

Hakan na zuwa ne duk yunƙurin gwamantin jihar da rundunar ƴan sanda na hana zuwan sanatar.

A baya ne dai rundunar ƴan sandan jihar ta fitar da sanarwar barazanar tsaro, inda ta yi kira ga dakatacciyar sanatar da ta janye batun gangamin da aka shirya da sunanta.

Yadda ta isa mazaɓarta
By Babaji