Alamu na nuna cewa ƴaƴan jam’iyyar PDP tsagin Mustapha Inuwa na shirin ficewa daga jam’iyyar nan bada jimawa ba.
A wani taron gaggawa da suka yi a Katsina ƙarƙashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin Katsina Mustapha Inuwa ya faɗa wa taron cewa nan bada dadewa zasu san matsayin su a jam’iyyar.
“Muna ta tuntuɓar mutanen mu da wasu ya’yan wasu jam’iyu a jihar da ƙasa baki ɗaya ƙarƙashin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar madugu a tafiyar kafin mu fidda matsaya”inji Mustapha Inuwa.
PDP a Katsina ta rabu gida biyu ne, akwai ɓangaren sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da ɓangaren Mustapha Inuwa,sai dai ita uwar jam’iyyar tuni ta amince da tsagin Lado Ɗanmarke.
Ganin yadda uwar jam’iyyar ta ƙasa ta ɗauki wannan hukunci,tsagin jam’iyyar na Mustapha Inuwa suka garzaya kotu sai dai basu samu nasara ba.
A taron da ya gudana akwai Sanata Ahmed Babba Kaita da tsohon sakataren jam’iyar ta ƙasa Sanata Ibrahim Tsauri da tsohon ɗan takarar mataimakin gwamna Ahmed Aminu Yar’adua da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP.
Waɗannan jigajigan ƴan jam’iyyar a jawabin su ga ɗunbin magoya bayan jam’iyyar sun ce, dole su nemawa kansu mafita a tafiyar siyasar su amma ba zasu ɗauki wani mataki ba, ba tare da sani sauran ya’yan jam’iyyar ba.
Alamu na nuna cewa akwai yiwuwar komawar su jam’iyyar SDP kamar yadda suke nunawa a cikin jawaban su sai dai lokaci zai nuna.
Jagora Mustapha Inuwa ya sanar da cewa suna tattaunawa da ya’yan jam’iyyun NNPP, PRP da wasu a cikin gwamnati mai ci yanzu.
Ya kuma yi kira ga magoya baya da su nuna juriya da hakuri kan ƙalubale da za su fuskanta a tafiyar.
